Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 16 a Adamawa
Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 16 a AdamawaDakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun ce sun kashe ’yan ta’adda 16 tare da kwato makamai a wasu samame da suka gudanar a Jihar Adamawa.A cewar rahoton…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 16 a Adamawa
Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun ce sun kashe ’yan ta’adda 16 tare da kwato makamai a wasu samame da suka gudanar a Jihar Adamawa.
A cewar rahoton Zagazola Makama, an gudanar da ayyukan tsakanin 30 ga Satumba da 1 ga Oktoba a yankin Sector 4.
Dakarun sun kashe ’yan ta’adda 16 a wani kwanton-bauna da suka yi a yankin Boima, Karamar Hukumar Gombi, inda suka kwato bindigogin AK-47 guda uku, bindigogin pump-action biyu da sauran kayan yaki.
Haka kuma, rundunar sojin sama ta kai hari kan wasu ’yan ta’adda 16 da aka gano tare da babura 15, inda rahoton ya ce harin ya samu inda aka nufa.
Sojojin sun kuma dakile hare-haren ’yan ta’adda kan bataliyar 226 da ke Garkida da ta 232 da ke Garaha.
Sai dai sojoji uku sun mutu yayin artabun, yayin da aka kwashe wadanda suka samu raunuka domin yi musu magani.
Rundunar ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike da samamen share yankunan da lamarin ya shafa, tare da kira ga jama’a da su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.
More from TimesPosts

Technology. ::: Ko Kunsan Mai yasa manta Shugaban Kasashe ke Rufe camera 📸 Idan Sunje Wajan Taro
Shin ko kasan dalilin da yasa manyan shugabannin ƙasashe suke sanya Tef ko Sticker a Camera 📸 ɗin wayoyin su a lokacin da suka halarci manyan taron ƙasashen duniya?. Malam this life is beyond your…
Ay Abdullahi2 min read

Wai Kunsa Mai Yake Faruwa A Kasuwar Cryptor Kuwa. ::: Labaran Duniya Cryptor
Wannan na cikin point da dazu nake making. Idan Bitcoin ya cigaba da faduwa har farkon January zai kakkarya patterns na shekaru da yawa. Sannan hakan zai leading to matsalar da Peter yake nunawa a…
Ay Abdullahi1 min read

Technology ::: Hackers hijacked digital billboards in Egypt, Malaysia and Brazil on Thursday to display sexually explicit videos, with claims of similar attacks in Iraq and China
Hackers hijacked digital billboards in Egypt, Malaysia and Brazil on Thursday to display sexually explicit videos, with claims of similar attacks in Iraq and China. In Giza, drivers on one of Cairo’s…
Ay Abdullahi1 min read