Nasiha ::: shin ko kunasa Wanna batu kuwa ...
JAN HANKALI: Ana yawan yaudarar matasa da sunan aiki a ƙasashen waje kamar Lìbya, Algeria, da wasu ƙasashe masu wahalar rayuwa. Ana kiran mutane da cewa "za a kai ka company" ko "akwai aiki wanda ake…
Ay Abdullahi · Admin
· 1 min read

JAN HANKALI: Ana yawan yaudarar matasa da sunan aiki a ƙasashen waje kamar Lìbya, Algeria, da wasu ƙasashe masu wahalar rayuwa. Ana kiran mutane da cewa "za a kai ka company" ko "akwai aiki wanda ake sumun kudi sosai. yawanci ƙarya ce! Yaudara ce! Tarko ne!
Ka sani cewa, kasarka ita ce gidanka kuma duk abinda kake nema a kasarka zaka iya samu idan Allah ya yarda, sai dai idan, rabonka daman a chan yake, inda za ka tafi, ba ka da yanci.
Inda kana da wata sana'a da kake yi anan gida gwara kayi hakuri ka rike da kyau, idan kayi hakuri ka dage wata rana zakayi nasara.
Chan idan zaka tafi, ba ka da dangi. Ba ka da wanda zai tsaya maka.
Muna kira ga duk wanda ke shirin tafiya ta hannun waɗannan agents:
Ka Tsaya Kayi Tunani Kayi Bincike akai
Kar ka bari a dauke ka daga ƙasarka har zuwa wurin da ba ka san komai ba. Kar ka bari a yaudare ka da alkawuran da ba su da tushe. Kar ka bar iyayenka da 'yan uwanka cikin dimuwa ba tare da sun san wani hali kake ciki ba.
Idan ka san wani Dan uwanka yana shirin tafiya irin wannan ka dakatar da shi, ka bashi shawara, da yayi hakuri ya cigaba da harkokinsa, har zuwa lokacin da Allah zai kawo masa mafita.
Rayuwa dai ɗaya ce.
Kar ka jefa ta cikin hadari saboda maganar wanda ya san ribarsa, ba rayuwarka ba.
A Kiyaye!
Allah Ubangiji Yasa Mu Dace Amin.
Daga Usman Tijjani Rijiyarlemo
More from TimesPosts

Labaran Duniya. ::: IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂
IRAN TA RIKITA AMURKA GABADAYA 😂Tsohon Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya bayyana cewa hanya daya tilo da Amurka za ta iya cin nasara ga Iran ita ce kai mata farmakin sojojin kasa,…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran chiki Gida Nigeria. :: Sarki Sanusi ya kai ziyara ga Olubadan a Ibadan don ƙarfafa alaƙar Hausawa da Yarabawa
Sarki Sanusi ya kai ziyara ga Olubadan a Ibadan don ƙarfafa alaƙar Hausawa da YarabawaMai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyara fadar Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, domin…
Ay Abdullahi1 min read

Labaran Duniya ::: Yau Shekaru 79 da Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga cikin manyan bindigogin kai hari na farko
Yau Shekaru 79 da Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga cikin manyan bindigogin kai hari na farkoA Ranar 13 Ga Watan Nuwamba 1947 Tarayyar Soviet ta kammala samar da AK-47, daya daga…
Ay Abdullahi3 min read